Sign in
Sign in
Sign in
Select Language
018

Al-Kahf 18:39 ولولا اذ دخلت جنتك قلت ما شاء الله لا قوة الا بالله ان ترن انا اقل منك مالا وولدا ٣٩

18:39
وَلَوۡلَآ
إِذۡ
دَخَلۡتَ
جَنَّتَكَ
قُلۡتَ
مَا
شَآءَ
ٱللَّهُ
لَا
قُوَّةَ
إِلَّا
بِٱللَّهِۚ
إِن
تَرَنِ
أَنَا۠
أَقَلَّ
مِنكَ
مَالٗا
وَوَلَدٗا
٣٩
"Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) bãbu wani ƙarfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi ƙaranci daga gare ka a wajen dũkiya da ɗiya."
Continue Reading

Read Tafsir

Ibn Kathir (Abridged)

The Response of the Poor Believer

Allah tells us how the rich man's believing companion replied to him, warning and rebuking him for his disbelief in Allah and allowing himself to be deceived.

أَكَفَرْتَ بِالَّذِى خَلَقَكَ مِن تُرَابٍ

(Do you disbelieve in Him Who created you out of dust...) This is a

…

The Response of the Poor Believer

Allah tells us how the rich man's believing companion replied to him, warning and rebuking him for his disbelief in A

…
More Tafsirs

Read in Context

Chapter 18, Page 298, Juz 15

32. Kuma ka buga musu misãli da waɗansu maza biyu. Mun sanya wa ɗayansu gõnaki biyu na inabõbi, kuma Muka kẽwayesu da itãcen dabĩnai, kuma Muka sanya shũka a tsakãninsu (sũ gõnakin). 33. Kõwace gõna daga biyun, tã bãyar da amfãninta, kuma ba ta yi zãluncin kõme ba daga gare shi. Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙoramu a tsakãninsu. 34. Kuma ɗan ĩtãce ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abõkinsa, alhali kuwa yanã muhãwara da shi, "Nĩ ne mafĩfĩci daga gare ka a wajen dũkiya, kuma mafi izza a wajen jama'a." 35. Kuma ya shiga gõnarsa, alhãli yanã mai zãlunci ga kansa, ya ce: "Bã ni zaton wannan zã ta halaka har abada." 36. "Kuma bã ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiĩna, to, lalle ne, zan sãmi abin da yake mafi alhẽri daga gare ta ya zama makõma." 37. Abõkinsa ya ce masa, alhãli kuwa yanã muhãwara da shi, "Ashe kã kãfirta da wanda Ya halitta ka daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyi, sa, an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum?" 38. "Amma ni, shĩ ne Allah Ubangijina, kuma bã zan tãra kõwa da Ubangijina ba" 39. "Kuma don me, a lõkacin da ka shiga gõnarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) bãbu wani ƙarfi fãce game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi ƙaranci daga gare ka a wajen dũkiya da ɗiya." 40. "To, akwai fãtan Ubangijĩna Ya ba ni abin da yake mafi alhẽri daga gõnarka, kuma ya aika azãba a kanta (ita gõnarka) daga sama, sai ta wãyi gari turɓãya mai santsi." 41. "Kõ kuma ruwanta ya wãyi gari faƙaƙƙe, sabõda haka, bã zã ka iya nẽmo shi ba dõminta." 42. Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itãcensa, sai ya wãyi gari yanã jũyar da tãfunansa biyu, sabõda abin da ya kashe a cikinta, alhãli kuwa ita tanã kwance a kan rassanta, kuma yanã cẽwa, "Kaitõna, dã dai ban tãra wani da Ubangijina ba!" 43. Kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, waɗanda ke taimakon sa, baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba. 44. A can taimako da jiɓinta ga Allah yake. Shĩ ne kawai Gaskiya, shĩ ne Mafĩfĩci ga lãda kuma Mafĩ fĩci ga ãƙiba.

- Abubakar Mahmood Jummi

Notes and Reflections

You do not have any notes or reflections on this verse.

Notes placeholders

Stay Connected to the Quran ❤️

Short meaningful reminders to reset, reflect and stay connected to the Quran.

Read, Listen, Search, and Reflect on the Quran

Quran.com is a trusted platform used by millions worldwide to read, search, listen to, and reflect on the Quran in multiple languages. It provides translations, tafsir, recitations, word-by-word translation, and tools for deeper study, making the Quran accessible to everyone.

As a Sadaqah Jariyah, Quran.com is dedicated to helping people connect deeply with the Quran. Supported by Quran.Foundation, a 501(c)(3) non-profit organization, Quran.com continues to grow as a free and valuable resource for all, Alhamdulillah.

Navigate
Home
Quran Radio
Reciters
About Us
Developers
Product Updates
Feedback
Help
Donate
Our Projects
Quran.com
Quran For Android
Quran iOS
QuranReflect.com
Quran.AI
Sunnah.com
Nuqayah.com
Legacy.Quran.com
Corpus.Quran.com
Non-profit projects owned, managed, or sponsored by Quran.Foundation
Popular Links
Duas from the Quran
Quran Verse of the Day
Ayatul Kursi
Yaseen
Al Mulk
Ar-Rahman
Al Waqi'ah
Al Kahf
Al Muzzammil
SitemapPrivacyTerms and Conditions
© 2026 Quran.com. All Rights Reserved
Contribute